Odion Ighalo ya koma ƙungiyarsa ta Shanghai Shenhua bayan yarjejeniyar zaman aronsa ta ƙare a Manchester United.
A watan Janairun 2020 ne dai United ta ɗauko tsohon ɗan wasan Nijeriyar a matsayin aro inda kuma ya fara taka leda a ƙungiyar da ƙafar dama, kafin cutar Covid-19 da ta tilasta dakatar da harkokin wasanni a watan Maris.
Ighalo ya ci wa United ƙwallaye biyar a wasanni 23 da ya buga mata.
