Home Labarai IGP ya ƙara jibge dakaru don nemo ɗaliban Kagara

IGP ya ƙara jibge dakaru don nemo ɗaliban Kagara

36
0

Babban Sifetan ‘yansandan Nijeriya Mohammed Adamu ya bada tabbacin rundunar a kokarin da take na ceto wadanda aka sace a harin da aka kai makarantar Sakandiren Kimiyya da ke Kagara, jihar Neja cikin koshin lafiya.

Adamu ya ce rundunar ta sake jibge karin jami’ai a jihar Neja, da za su tallafawa yinkurin sojoji da sauran jami’an tsaro wajen ceto mutanen.

Babban Sifetan ‘yansandan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Twitter na Rundunar a ranar Alhamis, kwana guda bayan sace dalibai da ma’aikatan makarantar da ‘yanbindiga suka yi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply