Babban Sufetan ‘yansandan Nijeriya Muhammad Muhammad Adamu ya sanar da soke sashen rundunar da ke dakile ayyukan ‘yan fashi a kasar baki daya.
Muhammad Adamu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin nan ya yin da ya ke jawabi ga manema labarai a Abuja.
Ko a farkon makon nan mai karewa an gudanar da zanga-zanga a wasu daga cikin manyan jihohin kasar nan, inda aka rika kira da a soke rundunar ta SARS.
