Home Labarai Ilimi: Jami’ar Abuja ta kori Malamanta guda biyu bisa zargin lalata da...

Ilimi: Jami’ar Abuja ta kori Malamanta guda biyu bisa zargin lalata da dalibai mata

98
0

Ahmadu Rabe

Bayanai sun nuna cewa hukumar gudanarwa ta Jami’ar Abuja ta sallami malamanta guda biyu bayan wani nazari da ta yi a kan wani rahoto na mutane takwas da ta kafa domin bincikar wadanda ake tuhuma da yin lalata da dalibai a jami’ar.

Jami’in hulda da jama’a a jamiar Dr. Habibu Yakubu ya ce jami’ar ta sallami Farfesa Adeniji Abiodun na sashen koyar da ilimin fasahar aikin gona da kuma Farfesa Agaptus Orji wanda ya ke koyarwa a tsangayar koyar da kimiyyar muhalli.

Bayan fitar da sanarwar ta korar malaman guda biyu, kazalika jami’ar ta kara fitar da wata sanarwa ta rage darajar wasu daga cikin malamanta guda biyu da ke wani sashe na daban ciki hada Robert Dajal daga matsayin Karamin Farfesa (Associate Professor) zuwa matsayin babban laccara (Senior Lecturer) sai kuma Mista Gana Emmanuel Sunday wanda aka rage wa matsayi daga babban lecturer zuwa matsayin mataimakin laccara bisa samun su da laifin aikata ba daidai ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply