Majalisar zartaswa ta kasa ta amince da wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna da wani kamfanin gine-gine mai zaman kan shi, inda kamfanin zai gyara dakunan kwanan dalibai a kwalejin akan kudi sama da naira miliyan 740.
Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ya yin zantawarsa da manema labarai bayan kamala taron majalisar zartaswa na mako-mako da ake gudanarwa a fadar Shugaban kasa.
Ministan ya kara da cewa wannan yarjejeniya da aka kulla da kamfanin za ta dauki kimanin shekaru goma sha hudu.
A karshe yace kamfanin zai ci gaba da lura da dakunan kwanan har zuwa lokacin da kamfanin zai mayar da kudin da ya zuba ya kuma fitar da ribar sa.
