Home Sabon Labari IMN: Dawowar Zakzaky daga Indiya ta haifar da cece-kuce a Nijeriya

IMN: Dawowar Zakzaky daga Indiya ta haifar da cece-kuce a Nijeriya

77
0

Daga Saleem Ashiru Mahuta

A cikin wata sanarwa da kungiyar yan Shia ta IMN ta aike wa kafafen yada labarai ciki har da DCL Hausa, Ibrahim Musa mai magana da yawun kungiyar ya ce gwamnatin Nijeriya ta yi duk mai yiwuwa wurin rikita tafiyar jagoransu kasar Indiya neman lafiya.

Ya ce jami’an tsaro na farin kaya a Nijeriya sun tasa keyar shugaban kungiyarsu ta IMN Ibrahim El-Zakzaky tare da Matarsa Zeenat bayan dawowar su daga kasar indiya a juma’ar nan.

El-Zakzaky da Matarsa sun sauka da misalin karfe 12 na rana ta jirgin Ethiopian Airlines a filin sauka da tashi na kasa da kasa na Nnamdi Azikwe.

Sai dai gwamnatin Nijeriya tun kafin yanzu ta musanta duk wani zargi da yan Shia suke yi. Ta ce jagoran yan shia ya nuna dabiun da ke alamta cewa ya je wani abu ne ba wai neman lafiya ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply