Shugaban rukunin Kamfanin Dangote Aliko Dangote, ya gode wa Shugaban Nijeriiya Bola Tinubu bisa matakan da ya ɗauka, ciki har da cire tallafin man fetur da kuma canja fasalin dokokin kasuwar canjin kuɗaɗen waje.
Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya da ke Legas, inda ya ƙaddamar da sayar da hannayen jari na farko ga jama’a (IPO) na kamfanin Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals.
Dan kasuwar ya kuma yaba da salon shugabancin Tinubu, yana mai cewa matatar Dangote na taimakawa wajen tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin.
Dangote ya ce: “Ina so in gode masa bisa ɗaukar matakai, ciki har da cire tallafin man fetur da kuma mayar da tsarin canjin kuɗi zuwa tsarin da kowa zai iya shiga…”
Ya ce Kamfanin Dangote Group zai ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnati domin bayar da gudunmawa wajen ci gaban Nijeriya.
Ya ce: “Saboda haka, muna matuƙar gode muku bisa shugabancinku, kuma za mu ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnati domin tabbatar da cewa mun mai da wannan ƙasa tamu ta zama babbar ƙasa, sannan mu taimaka wajen ganin Afirka ta zama babbar nahiya.”
Dangote, wanda ya taɓa zama shugaban kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya, ya kuma bayyana mamakinsa kan yadda kasuwar ta samu sauyi, yana mai cewa bai taɓa tsammanin za ta kai matsayin da take a yanzu ba.
Ya ce: “Ni ne shugaban wannan kasuwa a baya. Ko lokacin da nake gayyatar mutane domin su zo su taimaka min wajen sauya fasalin kasuwar, ta yadda za ta zama kasuwa mai daraja ta duniya, ban taɓa tunanin za ta kai wannan matsayi da ta kai a shekarar 2026 ba.”
Ya ƙara da cewa za a gudanar da wata babbar bikin ƙaddamarwa nan gaba, inda Shugaba Tinubu zai halarta.
Sayar da hannayen jarin matatar Dangote ga jama’a, wanda aka fara ranar Litinin, ya ƙunshi sabbin hannayen jari na yau da kullum guda biliyan 4.1, kan farashin Naira 525 kan kowane hannun jari. Mafi ƙarancin adadin hannayen jarin da mutum zai iya saya shi ne guda 10, waɗanda darajarsu ta kai Naira 5,250.
Ana sa ran za a rufe sayar da hannayen jarin a ranar 13 ga Oktoba, 2026, bisa sharuddan da ke cikin takardar bayanan sayar da hannayen jarin.
