Home Sabon Labari Ina mamakin yadda rashin tsaro ya dawo Nijeriya- Buhari

Ina mamakin yadda rashin tsaro ya dawo Nijeriya- Buhari

90
0

Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya ce ya yi mamakin yadda al’amura suka koma baya a bangaren tsaro a jihohin Arewa Maso Yammacin kasar da sauran sassa. Ya ce a lokacin yakin neman zabe “mun san akwai matsalar Boko Haram amma abin da ke faruwa a  yanzu abin mamaki ne”

Shugaban ya ce rashin tsaro ba wai batu bane na addini ko kabila ba, kutungwila ce kawai ake kitsa wa Nijeriya. Amma ya ce dole  gwamnati za ta kara tashi tsaye don ta murkushe matsalar tsaron. Ya ce hakkin gwamnati ne ta samar da tsaro; idan ba a samar da tsaro ba to yunkurinsu na bunkasa tattalin arziki ba zai yi nasara ba.

Buhari ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Naija wanda a baya-bayan nan gwamnati ta bayar da umarnin tura jiragen sama don magance ‘yan bindiga da suka addabi jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply