Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta musanta zargin da jam’iyyar NDC ta yi cewa hukumar ta cire wasu daga cikin ‘yan takarar da jam’iyyar ta tsayar a zaɓen 2027, tare da maye gurbinsu da wasu sunaye da jam’iyyar ba ta sani ba.
A cewar INEC, zargin ya fi shafar wasu mazabun majalisar dokokin jihar Anambra, inda NDC ta yi ikirarin cewa an sauya sunayen ‘yan takararta ba tare da izininta ba.
Babban sakataren yaɗa labaran shugaban hukumar INEC, Adedayo Oketola, ya ce hukumar ba ita ce ke tsayar da ‘yan takara a madadin jam’iyyu ba.
Ya bayyana cewa alhakin tsayar da ‘yan takara yana hannun jam’iyyun siyasa, matukar sun cika tanade-tanaden kundin tsarin mulki, dokar zaɓe ta 2026 da sauran dokoki, ƙa’idoji da jagororin da suka dace.
Mai magana da yawun shugaban na INEC ya ce zargin da NDC ta yi na cewa jami’an hukumar sun bi wasu ‘yan takara kai tsaye domin karɓar Form EC9, ba tare da izinin jam’iyyar ba, zargi ne mai matuƙar nauyi.
A cewarsa, NDC ta yi ikirarin cewa jami’an INEC sun karɓi bayanan wasu masu neman takara daga hannunsu kai tsaye, sannan suka ɗora bayanansu a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar ba tare da amincewar shugabannin NDC ba.
Sai dai INEC ta ƙalubalanci jam’iyyar da ta gabatar da hujjojin da ke nuna cewa wani jami’in hukumar ya shiga cikin irin wannan katsalandan da ba shi da izini.
Hukumar ta kuma nemi NDC ta bayyana sunayen jami’an da take zargi tare da gabatar da duk wasu hujjoji da za su tabbatar da zargin nata.
INEC ta ce idan jam’iyyar ta gabatar da sahihiyar hujja kan rashin da’a da wani jami’inta ya aikata, za ta gudanar da bincike bisa tsarin da aka tanada.
Hukumar ta jaddada cewa ba ita ce ke zaɓar ko tsayar da ‘yan takarar jam’iyyu ba, sai dai aikinta shi ne tabbatar da cewa waɗanda jam’iyyun suka gabatar sun cika sharuddan da doka ta tanada.
Lamarin ya zo ne yayin da ake ƙara samun shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027, musamman kan batun tantancewa da fitar da jerin sunayen ‘yan takarar jam’iyyun siyasa.
