Home Labarai INEC za ta ƙirƙiro sabbin rumfunan zabe

INEC za ta ƙirƙiro sabbin rumfunan zabe

42
0

Hukumar Zaben Nijeriya mai zaman kanta ta (INEC) ta ce tuni ta fara aikin samar da karin rumfunan zabe (PUs) a dukkanin mazabun da ke fadin kasar.

Kwamishina a hukumar zaben kuma shugaban kwamitin yada labarai da ilmantar da masu zabe, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja a karshen taron gudanarwar hukumar.

A watan Agustan shekarar 2014 ne hukumar ta INEC ta gabatar da shawarar kirkirar karin rumfunan zabe 30,027 a fadin kasar.

Sai dai majiyar DCL Hausa ta ce yankin arewa zai fi samun kaso mafi yawa na sabbin rumfunan zaben da za a kirkira, inda za a kirkiri sabbin rumfunan har guda 21,615 a Arewa.

Yayin da yankin kudancin kasar nan zai samu sabbin rumfunan zaben guda 8,412.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply