Home Sabon Labari INEC za ta je kotun koli kan soke rijistar wasu jam’iyyu

INEC za ta je kotun koli kan soke rijistar wasu jam’iyyu

127
0

Hukumar zaben Nijeriya  INEC ta ce ta shirya tsaf domin garzayawa kotun koli game da wasu hukunce-hukunce masu karo da juna da kotun daukaka kara ta yanke akan ikon da hukumar take da shi na soke rijistar wasu daga cikin jam’iyyun siyasa a kasar.

Kwamashinan hukumar kuma mai kula da sashen watsa labarai da kuma wayar da kan masu zabe Mr Festus Okoye ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da aka rarraba ga manema labarai a Abuja.

Sanarwar dai ta bayyana cewa jam’iyyun siyasa 74 ne aka soke rijistar su sakamakon gazawar su wajen cika ka’idojin da kundin tsarin mulkin kasar  ya tanadar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply