Home Labarai INEC za ta samar da karin runfunan zabe

INEC za ta samar da karin runfunan zabe

164
0

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce za ta samar da karin runfunan zabe don fuskantar zaben shekarar 2023.

Shugaban INEC Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin zaman gyara kundin zaben da kwamitocin majalisar dokoki suka gabatar.

Shugaban na INEC ya bayyana cewa yinkurin samar da sabbin runfunan na cikin kudirinsa don ganin an ragewa masu zabe wahala yayin kada kuri’unsu.

Tunda fari, shugaban kwamitin gyaran kundin zaben, Sanata Kabir Gaya ya bayyana cewa kwamitin nasa ya samu korafe korafe 35 da ake bukatar a gyara a kundin zaben.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply