Rahotanni daga kasar Iran na cewa mutane 35 ne suka mutu a safiyar yau Talata a yayin jana’izar Soleimani Qassem.
Kafar yada labarai ta Aljazeera ta ce mutuwar mutanen ta faru ne sakamakon turmutsitsi da aka samu a wurin jana’izar Qassem a mahaifarsa da ke kasar Iran. Duban dubatar yan kasar ta Iran ne suka halarci jana’izar don yin bankwana da shi.
A ranar Juma’a ne dai kasar Amirka ta yiwa Janar din sojan kisan gilla a wani hari da tai na jirgin sama.
A yanzu tuni danganta tsakanin Amirka da Iran ta kara yin tsami. Jama’ar kasar Iran na yin machi suna cewa a yi harin ramuwar gayya, yayinda shugaban Amirka Donald Trump ke cewa idan har Iran ta kuskura ta kai musu hari to Amirka za ta mayar da martani da kai mata hari a wurare sama da 50.

Allah ya yayyafama fitina ruwan sanyi