Home Coronavirus Iran ta fara gwajin rigakafin Covid-19 da ta samar

Iran ta fara gwajin rigakafin Covid-19 da ta samar

70
0
Lokacin da wata Jami'ar jinya ke yin allurar rigakafin ga wata da ta sadaukar da kanta don a yi gwajin allurar a kanta

Kasar Iran ta fara gwajin allurar rigakafin cutar COVID-19 da ta sana’anta a cikin gida.

A ranar Talatar nan aka yi wa wasu mutum 3 allurar rigakafin mai suna Coviran Barekat, a gaban Ministan Lafiyar kasar.

Karin wasu mutum 56 kuma za su karbi allurar, wanda shi ne matakin farko na gwajin rigakafin kafin a fitar da sakamako a cikin wata daya.

Shugaba Hassan Rowhani ya ce Iran za ta yi amfani da rigakafin COVID-19 da aka sana’anta a kasashen waje da kuma na cikin gida.

Iran na fama da matsala wajen shigo da rigakafin cutar daga waje, saboda takunkumin da Amirka ta sanya mata, wanda ya sa ba ta iya yin huldar banki wajen yin cinikayya da wasu kasashe.

Duk da haka, Babban Bankin Iran ya ware akalla Dala miliyan 245 domin shigo da rigakafin daga kasashen waje.

Sai dai kuma a kullum kimanin mutum 6,000 ne ke kamuwa da ita, 120 kuma take yin ajalinsu a kasar.

Daga lokacin da cutar ta fara bulla zuwa yanzu, ta kashe mutum 54,000 daga cikin mutum miliyan 1.2 da suka kamu da ita a Iran.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply