Home Kasashen Ketare Iraqi ta kashe ‘yan ta’adda 21 ta hanyar rataya

Iraqi ta kashe ‘yan ta’adda 21 ta hanyar rataya

129
0

Kasar Iraqi ta kashe mutane 21 da aka samu da laifin aikata ta’addanci ta hanyar rataya.

Majiyar jami’an lafiya da ta ‘yansanda ta ce an fara tuhumar mutanen tun a shekarar 2005 karkashin dokar hana ta’addanci, amma dai ba a bayyana hakikanin lafukansu ba.

An dai rataye su a gidan yarin Nasiriyya a lardin Dhi Qar.

Tun dai bayan ayyana cewa an yi galaba kan kungiyar IS a 2017, kasar Iraqi ta ke aiwatar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da hannu a kungiyar IS.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply