Home Coronavirus Italiya: Silvio Berlusconi ya kamu da corona

Italiya: Silvio Berlusconi ya kamu da corona

106
0

Tsohon Firai Ministan Italiya, Silvio Berlusconi, mai shekara 83, yana asibiti domin yin jinyar cutar sankarar huhu, kana daga bisani gwaji ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar corona.

Rahotanni daga kafafen watsa labaran kasar sun ce tuni aka killace Mista Berlusconi inda ya ke samun kulawa ta musamman daga likitocin asibitin.

Silvio Berlusconi dai attajiri ne kuma dan siyasar da ya shahara a kasar Italiya, shi ne wanda ya yi aiki a matsayin Firai Ministan Italiya da gwamnatoci hudu da suka mulki kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply