Home Labarai Iyaye sun yi zanga-zangar yawaitar ɓatan yara a Kano

Iyaye sun yi zanga-zangar yawaitar ɓatan yara a Kano

54
0

Iyayen yara mata da dama ne da yaransu suka ɓace, suka gudanar da zanga-zanga a jihar Kano, don nuna ɓacin ran su kan abun da suka kira halin ko in kula da hukumomi ke nuna wa, wajen ganin an nemo yaransu.

Matan, waɗanda ke riƙe da kwalaye da ke ɗauke da rubutu da hotunan yaran da suka ɓata, sun je hukumar karɓar koken jama’a ta jihar da kuma Ma’aikatar Harkokin Mata domin miƙa buƙatarsu.

A dukkan wuraren, shugabar tawagar Zainab Abdullahi Giginyu, ta ce abun da ya dake su shi ne, tsawon shekaru suna ƙorafi kan batun amma har yanzu gwamnati ta ƙi yin abun da ya dace.

Da suke jawabi ga masu zanga-zangar, Kwamishinan Harkokin Matan jihar Zahara’u Muhammad da kuma Shugaban hukumar sauraron koken jama’ar Barrister Muhuyi Rimin Gado, sun ba matan tabbacin gwamnatin jihar, na yin duk abun da za ta iya, na ganin yaran sun dawo ga iyayen su.

Ɓatan yara dai ba wani sabon abu ba ne a jihar Kano, yadda aka daɗe ana fama da shi, saidai an sha kama waɗanda ake zargi da satar yaran tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply