Home Kasashen Ketare Jakada Libya a majalisar Dinkin Duniya ya yi murabus

Jakada Libya a majalisar Dinkin Duniya ya yi murabus

66
0

Wakilin Libya na musamman a majalisar dinkin duniya ya yi murabus, saboda abunda ya kira kokarin tabbatar da zaman lafiya a kasar da ke arewacin Afrika na yin illa ga rayuwar sa.


Ghassan Salame, ya rubuta a shafin san a Twitter cewa ya shafe kimanin shekara biyu da rabi yana kokarin hada kan Libya tare kokarin ganin kasashen waje ba su shigo cikin rikicin kasar ba.
Saidai kuma, ya ce yanayin lafiyar jikin sa ba zai bar shi ci gaba da wannan aiki mai matukar gajiyarwa ba, a don haka ya bukaci sakataren majalisar dinkin duniya, ya sauwake masa.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ofishin jakadancin majalisar dinkin duniya a Libya da kuma ofishin majalisar da ke Geneva ba su ce komai ba a kan batun.
A makon da ya gabata ne dai, Salame ya gayyaci bangarorin gwamnatin National Accord mai samun goyon bayan majalisar dinkin duniya, da kuma Genaral Khalifa Haftar domin tattaunawar zaman lafiya a birnin Geneva amma kuma wakilan bangarorin biyu suka dakatar da shiga tattaunawar.
Wannan dai ya kawo tsaiko wajen kawo karshen rikicin kasar da ake fama da shi tun a shekarar 2011 lokacin da aka hambarar da Muammar Gaddafi.
A cikin watan janairu ne dai kasar Turkey ta aiwatar da wata doka mai cike da sarkakiya don jibge dakarunta da za su taimakawa gwamnatin kasar a Tripoli, Qatar ma, na goyon bayan gwamnatin kasar ta Firaminista Fayez Al-Sarraj.
Kasashen Masar, Russia, Saudiyya da Daular Larabawa kuwa na nuna goyon bayan su ne ga mayakan Haftar da ke rike da akasarin gabacin kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply