Jakadan Nijeriya a kasar Amurka Sylvanus Nsofor ya mutu yana da shekaru 85.
Duk da dai cewa ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance, amma dai wata majiya mai tushe ta tabbatar da mutuwar tasa ga jaridar Thisday
A shekarar 2017 ne Ambassada Nsofor ya fara aiki a matsayin jakada.
Ya dai gaji Prof Adebowale Adefuye wanda shi ma ya mutu yana dab da kammala wa’adin mulkinsa na jakadan Nijeriya a Amurka.
