Home Labarai Jama’a sun kashe ƴanbindiga shida a taron dangi, a Kaduna

Jama’a sun kashe ƴanbindiga shida a taron dangi, a Kaduna

222
0

Wani rahoto kan tsaro da aka gabatarwa gwamnatin Kaduna a ranar Juma’a, ya nuna cewa mazauna ƙananan hukumomin Sanga da Lere sun yi nasarar kashe ƴanbindiga shida a lokuta daban-daban.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, ya ce a ranar Alhamis ne wasu ƴanbindiga suka kai hari a garin Fadan Karshi dake ƙaramar hukumar Sanga, inda suka yi wa wani ɗan kasuwa fashi, saidai mutanen garin sun far masu tare da ƙone biyu daga ciki har lahira.

Kuma dai da yammacin ranar ne wasu ƴanbindigar suka tare hanyar Aboro zuwa Kafanchan har suka harbi wani direba, wanda shima ya buge ɗaya daga cikin ƴanbindigar har lahira.

Aruwan ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun basu rahoton cewa ƴanbindiga da suka shigo daga wata jiha maƙwabciya sun far wa ƙauyen Domawa da ke ƙaramar hukumar Lere, saidai jama’ar ƙauyen sun tasar masu inda suka kashe uku daga cikinsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply