Home Labarai Jama’ar ƙauye 143 rashin tsaron kudancin Kaduna ya raba da gidajensu

Jama’ar ƙauye 143 rashin tsaron kudancin Kaduna ya raba da gidajensu

38
0

Kungiyar jama’ar Kudancin Kaduna SOKAPU, ta ce al’ummomi 143 a kananan hukumomin yankin, rashin tsaro ya raba da muhallansu.

Da yake magana da ‘yanjarida a Kaduna, shugaban kungiyar Jonathan Asake, ya ce sama da mutum dubu 160, wadanda yawancinsu mata ne da kananan yara ke rayuwa a cikin matsananciyar rayuwa ta rashin abinci, kiwon lafiya da duk sauran wasu abubuwan more rayuwa.

Ya kuma kara dacewa jama’ar yankin na Kudancin Kaduna sun yi asarar da ta kai sama da Naira miliyan 900 tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2020.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply