Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta Nijeriya JAMB, ta yi gargadi kan samuwar cibiyoyin shirya jarabar ta kwamfuta masu bada satar amsa.
Magatakardan hukumar Farfesa Ishaq Oloyede ya ce karuwar irin wadannan cibiyoyi a yankin Arewa, ya nuna yadda matsalar ta yi kaura daga kudanci zuwa Arewacin kasar.
Oloyede wanda ya bayyana haka a lokacin wani taron ‘yan jarida a Abuja, ya ce yanzu haka sama da dalibai 400 da ke neman shiga jami’o’i da manyan makarantun kasar aka kama da satar amsa.
Ya kuma yi zargin cewa akwai wasu manyan makarantu da ke goyon bayan wannan matsala.
