Home Coronavirus Jamhuriyar Nijar ta bude makarantu a hukumance

Jamhuriyar Nijar ta bude makarantu a hukumance

111
0

A wannan Litinin ne a dukkan fadin kasar jamhuriyar Nijar daliban makarantun boko suka sake komawa azuzuwa.

Kamar dai ko ina a kasar a nan Damagaram ma Gwamnan jihar Isa Musa ya jagoranci kaddamar da komawar a cikin makarantar Mela Douaram.

An koma wannan makarantu ne dai a cikin yanayin matakkan rigakafin cutar Covid-19 da suka hada da tanadar wuraren wanke hannaye a cikin makarantun da raba takunkumin rufe hanci da baki ga kowane dalibi sai kuma sanya tazara a tsakanin daliban a cikin ajijuwan da ma a harabar makarantun.

Hotan wani aji da aka bude cikin bin matakan tazara

Wannan mataki dai na bude makarantun ya biyo bayan samun sauki da aka yi na yaduwar wannan cuta da ta tilasta a baya daukan matakin rufe su har na tsawan sama da watanni biyu

A yanzu dai abin jira a gani shine idan har kwanakin 45 da za’a yi nan gaba zai bada damar idasa karantun shekarar duba da yadda wasu daliban ke ganin kwanaki sun yi kadan a kammala darasun da ya rage

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply