Home Labarai Jami’an EFCC sun yi awon-gaba da tsohon gwamnan jihar Zamfara

Jami’an EFCC sun yi awon-gaba da tsohon gwamnan jihar Zamfara

105
1

Abdullahi Garba Jani

Jaridar Daily Nigerian ta rawito cewa jami’an hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati EFCC sun yi awon-gaba da tsohon gwamnan jihar Zamfara Mahmuda Shinkafi.

Da misalin karfe daya na rana ne dai aka ba da rahoton cewa jami’an sun isa gidan tsohon gwamnan da ke kan titin Nagogo a Kaduna, suka yi awon-gaba da shi.

Wata majiya ta kusa-kusa da ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da kama shi. Majiyar ta ce iyalansa ba su san inda aka nufa da shi ba.

Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar EFCC, ya ce a dan ba shi lokaci kafin tantance lamarin.

A ranar Alhamis ne dai aka gabatar da sunayen shaidu guda 3 a shari’ar da ake gudanarwa ta tsohon ministan Kudi Bashir Yuguda, da suka hada da tsohon gwamna Mahmuda Aliyu Shinkafi, Aminu Ahmad Nahuche da Ibrahim Mallaha a gaban mai shari’a Fatima Adamu ta babbar kotun tarayya da ke Gusau.

EFCC dai na tuhumarsu da zargin amsar Kudi Naira milyan 450 daga tsohuwar ministar albarkatun man fetur Mrs Diezani Alieson Madueke da nufin jan ra’ayi a zaben 2015.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

  1. Muna gayyatar hukumar EFCC a karamar hukumar Mani ta jihar katsina data gudanar da bincike akan Dan majalissa mai wakiltar karamar hukumar Mani abisa kudi naira milyan Biyar. Na kudin maaikatan zaben 2019

Leave a Reply