Hukumar Hisbah ta jihar Bauchi ta kwace kiret 260 na giya daga otal da gidajen casu a yunkurinta na ganin ta tsaida shari’a a jihar.
Kwamishinan kula da gudanar da Hisbah da Shari’a Malam Aminu Balarabe ya bayyana hakan yayin da yake nuna kayan ga ƴanjarida a garin Bauchi a ranar Talatar yau.
Ya bayyana cewa sun kama 216 ne a karamar hukumar Misau, 44 kuma a wani gidan giya dake cikin garin Bauchi da wasu kuma a kusa da Dass.
Ya kuma shaida cewa hukumar tasa ba ta buƙatar izinin kotu wajen lalata kayan kamar yadda dokar 2003 ta hana sha ko fataucin kayan maye a jihar ta tanadar.
Majiyar DCL Hausa ta shaida cewa a ƴan kwanakin baya hukumar ta Hisbah ta kama wasu matasa da suka shirya casun tsiraici a karamar hukumar Tafawa Balewa.
