Home Labarai Jami’an Rigakafi sun samu kyautar Babura da kwamfutoci a Nasarawa

Jami’an Rigakafi sun samu kyautar Babura da kwamfutoci a Nasarawa

163
0

Hukumar bunkasa kiwon lafiya a matakin farko ta jihar Nasarawa (NAPHDA) ta raba babura 26 da kwamfutar tafi-da-gidanka guda 26 ga jami’an rigakafi.

Shugaban hukumar na jihar Dr. Mohammed Usman Adis ne ya sanar da haka yayin da yake bayar da wadannan kayayyakin ga jami’an riga kafin, ya ce “ina kira gareku da ku yi amfani da babura da kwamfutar kamar yadda doka ta tanada.”

Kazalika, ita ma Shugabar Tsare-tsaren hukumar NAPHCDA, Misis Nnenna Eze, ta yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da wadannan kayayyakin don yi wa al’ummar jihar hidima.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply