Kulob din Manchester United ya ce yana da masaniyar abin da ya faru da kyaftin dinsa Harry Maguire a daren Alhamis a Mykonos na kasar Girka.
Dan wasan baya na kasar Ingila mai shekaru 27, an ba da rahoton cewa jami’an tsaro sun yi awon-gaba da shi bayan wani lamari da ba a bayyana ba ya faru da dare.
‘Yan wasan Man U dai na dan sararawa bayan fitar da su da Sevilla ta yi a gasar Europa League.
