Home Labarai Jami’ar Amirka ta nemi yafiyar Ganduje

Jami’ar Amirka ta nemi yafiyar Ganduje

125
0

Jami’ar East Carolina ta Amirka ta ba gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje haƙuri kan duk wani cecekuce da rikicin batun naɗin da aka ce jami’ar ta yi masa ya janyo.

A cikin wata takarda wadda shugaban sashen ilimi na jami’ar Dr B. Grants Hayes ya fitar ɗauke da kwanan watan 8 ga watan Disamba, kuma aka aike wa Gwamnan, jami’ar ta ce ba ta da nufin yin duk wani abu da zai taɓa mutuncin gwamnan.

Takardar da jami’ar ECU ta aike wa Ganduje

Tun da farko dai sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ne ya buƙaci jami’ar ta bada haƙuri kan cin zarafin da soke naɗin da jami’ar ta yi wa Ganduje ya janyo.

Jami’ar ta Amirka, ta ce gwamna Ganduje ya mallaki dukkan wasu sharudɗa da takardun da ake buƙata da waɗanda aka ba matsayin suke da shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply