Jami’ar tarayya ta Birnin Kebbi, ta sanya ranar Litinin 18 ga watan Janairu a matsayin ranar da ayyukan koyo da koyarwa za su ci gaba a jami’ar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun jami’ar Jamilu Magaji ya fitar, ya ce amincewa da sake bude makarantar ya zo ne a lokacin taron majalisar zartaswar jami’ar karo na 22 da ya gudana a ranar Alhamis.
Shugaban jami’ar Farfesa BB Shehu ya ce hukumar gudanarwar jami’ar za ta sanya dokar hana shiga ga duk wanda bai da takunkumin rufe fuska.
A don haka ya yi kira ga jama’a su bada hadin kai ga ka’idojin da jami’ar za ta gindaya na kula da tsabtar kai da kuma sharuddan kariya daga cutar covid-19.
