Home Labarai Jami’in hukumar EFCC ya sha maganin kashe kwari ya mutu

Jami’in hukumar EFCC ya sha maganin kashe kwari ya mutu

67
0

 

Hannatu Mani Abu/Jani

 

Wani jami’in hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya ya kashe kansa ta hanyar shan maganin kashe kwari mai suna Sniper. Mr William Oyibogare wanda ya aikata wannan aiki na daga cikin jami’an hukumar da ke bangaren tattara bayanan sirri.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa an gano gawarsa ne da misalin karfe 7 na safiyar Juma’a a gidansa da ke Unguwar Giwa Amu a Benin babban birnin jihar Edo.

Majiyar jami’an tsaro ta ce wani abokin aikin Mr William ne ya ga gawarsa a lokacin da ya ziyarci gidansa don bin bahasin dalilin rashin zuwansa wurin aiki a ranar Alhamis, kuma ana ta kiran wayarsa ba a dauka.

Jaridar Daily Nigerian ta ba da labarin cewa da ‘yansanda suka je suna binciken musabbabin mutuwarsa ne suka samo wata wasiyya da ya rubuta, da kwasu kwayoyin magani da kuma maganin kashe kwari mai suna Sniper.

An dai kai gawarsa a dakin adana gawa na babban asibitin birnin Benin don ci gaba da bincike.

Har ya zuwa lokacin hada labarin nan dai, mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren bai dauki waya ko mai do sakon text da aka yi ma sa ba kan lamarin.

A ranar 20 ga watan Yuli 2019, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta hana sayar da maganin kashe kwari na Sniper kuma ta ba da umurnin da a janye shi a kasuwanni, biyo bayan yawan korafe-korafen da ake samu na shan sa don kashe kai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply