Jam’iyyar APC ce za ta ci gaba da mulkin Nijeriya har bayan 2031 – Abdulaziz Yari
Sanata Abdul’aziz Yari, sabon daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027, sannan jam’iyyar za ta ci gaba da riƙe mulkin ƙasar bayan shekarar 2031.
Yari ya bayyana hakan ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, jim kaɗan bayan dawowarsa daga ƙasar waje, inda magoya bayan jam’iyyar suka tarbe shi tare da yi masa addu’ar samun nasara a sabon aikin da aka ɗora masa.
Ya ce APC za ta samu nasarar sake zaɓar Tinubu ne bisa la’akari da ayyukan da gwamnatin ta gudanar cikin shekaru uku da suka gabata, tare da tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa jam’iyyar za ta cika alkawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.
“Da yardar Allah, Bola Ahmed Tinubu zai kasance shugaban ƙasa a 2027. Ina tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa duk alkawuran da muka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe za mu cika su,” in ji Yari.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba Tinubu hikimar jagorantar ƙasar, yana mai cewa APC za ta yi ƙoƙarin ganin ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da ke jagorantar Nijeriya bayan wa’adin Tinubu na biyu.
Sai dai wannan tabbaci na Yari ya zo ne a daidai lokacin da aka fara samun cece-ku-ce kan wasu daga cikin sunayen da aka saka cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027, musamman mutanen da ake zargin suna fuskantar wasu batutuwan tuhume-tuhumen rashawar da ba a warware su ba.
An dai bayyana Tinubu a matsayin shugaban kwamitin, yayin da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, suke daga cikin manyan jami’an kwamitin. Gwamnan Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma, an naɗa shi sakataren kwamitin, yayin da Yari ya zama darakta-janar na kwamatin gangamin nema wa Tinubu goyon bayan jama’ar Nijeriya a zaɓen na 2027.
