Jam’iyyun adawa na shirin haɗa kai gabanin zaben 2027 domin kayar da Tinubu a cewar rahoton da jaridar Daily Trust ta tattaro.
Manyan jam’iyyun adawa a Nijeriya na shirin haɗa ƙarfi domin tunkarar shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ƙungiyar G-100 ce ke jagorantar yunƙurin, inda take son haɗa ADC, PDP, NDC, PRP, SDP da APM, tare da samar da ɗan takarar da zai samu goyon bayan jam’iyyun.
Daga cikin ‘yan takarar akwai Atiku Abubakar, Peter Obi, Seyi Makinde da Donald Duke, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai yunƙurin na iya fuskantar ƙalubale sakamakon bambancin ra’ayoyi da burin shugabannin jam’iyyun.
Kungiyar ta G-100 dai na shirin gudanar da taron tattaunawa a ranar 18 ga Agusta domin neman matsaya guda, bayan irin wannan yunƙuri ya gagara samar da haɗin kai a baya.
