Home Kasashen Ketare Jamus ta samu rarar sama da Naira Tiriliyan 5 daga kasafin kudin...

Jamus ta samu rarar sama da Naira Tiriliyan 5 daga kasafin kudin 2019

85
0

Ministan kudin tarayyar Jamus Mr Olaf Scholz ya sanar a ranar Litinin cewa kasarsa ta samu rarar kudi da suka kai Dalar Amirka Bilyan 15, kwatankwacin sama da Tiriliyan 5 na Naira a kasafin kudi na shekarar 2019.

Wadannan kudade dai an same su ne ta hanyar karbar haraji da kuma kudin ruwa da masu biyan bashi ke bayarwa.

Duk da albashi da ayyuka na raya kasa da gwamnatin Jamus ta aiwatar a shekarar 2019, kasar ta sake samun rarar kudin  da kawo yanzu mahukumta basu san abin da za su yi da kudin ba.

Sai dai kawo yanzu an fara muhawara a kan ko a yi amfani da kudaden wurin kara samar da abubuwan more rayuwa.

Sashen Turanci na DW ya ruwaito Ministan Kudi Mr Olaf yana cewa sirrin tara wadannan kudade shi ne sun yi tsantseni kuma ba su yi facaka da kudin mutane ba.

Shekaru biyar ke nan a jere Jamus ta na samun rara daga cikin kudaden da take warewa a matsayin kasafin kudi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply