Home Coronavirus Janar Buratai ya killace kansa saboda zullumin kamuwa da corona

Janar Buratai ya killace kansa saboda zullumin kamuwa da corona

205
0

Shugaban rundunatr sojojin kasa ta Nijeriya  Tukur Yusuf Buratai tare da wasu manyan hafsoshin sojin kasar sun killace kansu  daga yanzu har zuwa  kwanaki 14 masu zuwa . Zullumin yaduwar coronar a tsakanin manyan hafsoshin sojin kasar ya yi kamari ne bayan da a ranar Alhamis rundunar sojin ta sanar da cewa wani babban soja ya kamu da corona, wanda acewar jaridar Dailytrust daga baya aka gano cewa Janar Johnson Olu Irefin wanda kuma cutar ta yi ajalinsa, duk da cewa a hukumance sojojin ba su ce shi ne ba.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar sojin Nijeriya Birgediya Janar Sagir Musa ya fitar ya ce an dakatar da taron manyan hafsoshin sojin kasa, Army Conference, na wannan shekara saboda an samu babban jami’in da ya halarci taron da cutar corona. A gefe guda kuma Shugaban rundunar sojin ta Nijeriya Tukur Buratai ya sanar da cewa ba zai samu damar halartar bikin dansa,Hamisu Tukur Buratai da aka tsara gudanarwa a wannan Jumma’a ba. Sai dai ya ce za a ci gaba da bikin kamar yadda aka tsara amma yana kira ga duk wanda ya san ya halarci taron Army Conference 2020 da kada ya halarci bikin d’an nasa, saboda da zullumin bazuwar corona a wurin taron da aka dakatar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply