Home Coronavirus Jaririn da ya kamu da Covid-19 a Kaduna ya warke

Jaririn da ya kamu da Covid-19 a Kaduna ya warke

102
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa an sallami jaririn nan ɗan wata huɗu da ya kamu da cutar Covid-19.

Jaririn dai yana daga cikin mutane 20 da aka tabbatar sun kamu da cutar a ranar 18 ga watan Mayu.

A bayanan da Kwamishinar lafiya ta jihar Dr Amina Mohammed Baloni ta bayar a ranar Asabar, gwamnatin jihar ta ce mutum 232 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, 149 sun warke, bakwai sun mutu, sai 76 da suka rage masu ɗauke da cutar.

Saidai Kwamishinar ta yi gargaɗin cewa, duk da an gudanar da gwajin kimanin mutum 2000, akwai yiwuwar yawan masu ɗauke da cutar zai iya ƙaruwa a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da gwajin cutar a wurare daban daban.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply