Home Labarai Jiga-jigan PDP sun gudanar da taron gaggawa

Jiga-jigan PDP sun gudanar da taron gaggawa

126
0

Jiga-jigan jam’iyyar PDP sun gudanar da wani taro a daren jiya Laraba, kafin taron majalisar zartaswar jam’iyyar da za a gudanar yau Alhamis.

Duk da cewa babu masaniya ga abun da aka tattauna a taron, saidai ana sa ran ficewar gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi daga PDP zuwa APC na ɗaya daga cikin batutuwa da taron ya ƙunsa.

Daga cikin mahalarta taron akwai gwamnonin Bauchi, Bayelsa, Abia, Akwa Ibom, Edo, Delta, Sokotoda Adamawa.

Haka ma tsohon shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da tsohon mataimakinsa Ike Ekweremadu, da tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Maƙarfi na cikin mahalarta taron, tare da shugaban jam’iyyar Uche Secondus.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply