Home Sabon Labari Jihar Delta: Gwamnati ta haramta malami ya sa dalibai aiki

Jihar Delta: Gwamnati ta haramta malami ya sa dalibai aiki

172
0

A jihar Delta dake yankin Niger Delta na Nijeriya daga yanzu gwamnati ta haramta wa malaman makarantun furamare da sakandire na gwamnati sanya dalibai aiki a lokacin da ake jarabawa.

A bisa ala’ada dai a makarantun gwamnati na Nijeriya malaman makarantu kan sa dalibai aikace-aikace irinsu shara da debo ruwa da noma da sauran aikace-aikace koda kuwa a lokacin daukar darasi ne.

A wasu lokuta daliban da suka yi laifi ne ake sa irin wadannan ayyukan, amma wasu lokutta ko dalibi yayi laifi ko bai yi ba za’a sanya shi domin abin da a ganin malamin ka iya sanya masa tarbiyya.

Sai dai kuma a jihar Delta kwamishinan ilimi a matakin farko da sakandire, Chief Patrick Ukah, ya ce daga yanzu ya haramta malamai da shugabannin makarantun gwamnati sanya dalibai irin wadanann ayyuka madamar ana gab da fara jarabawa.

Kwamishinan kamar yadda jaridar New Nigerian Newspaper ta ruwaito ya ce daukar wannan mataki ya zama wajibi don taimakawa dalibai samun sukunin yin karatun cin jarabawa da fahimtar abin da ake koya musu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply