Home Sabon Labari Jihar Edo: PDP mai adawa za ta sasanta rikicin jam’iyyar APC mai...

Jihar Edo: PDP mai adawa za ta sasanta rikicin jam’iyyar APC mai mulki

68
0

Daga Hannatu Mani Abu

Jam’iyyar PDP a jihar Edo ta shirya tsaf domin yin sasanci tsakanin gwamnan jihar Obaseki Godwin na jam’iyyar APC da uban gidan sa Adams Oshiomole wanda kuma shine shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya kuma tsohon gwamna a jihar ta Edo.

Oshiomole da Obaseki

Mr.Chris Nehaire mai magana da yawun jam’iyyar PDP a jihar dake kudu maso kudancin Nijeriya ya ce jam’iyyar PDP ba za ta zura ido akan barakar da ke faruwa tsakanin wadannan manyan mutane ba. Ya ce sulhun ta su ya zama wajibi domin ceto jihar daga kunyata a idon duniya.

A cewar sa “zamu samu lokaci da wuri domin tattaunawa tare da warware matsaloli dake faruwa tsakanin mutanen biyu zamu kuma tabbatar sunyi abin da ya dace suyi.”

Nehaire ya ce fifita muradun jihar Edo shine gaba da komai domin kuwa wannan hatsaniya ba za ta haifar wa jihar da da mai ido ba.

Idan za’ a iya tunawa a kwanan baya dai kakakin majalissar jihar ta Edo Mr. Frank Okiye ya fito karara ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole na neman dagula musu majalissa akan akan abin da ya nuna a matsayin son zuciya. Tun daga lokacin ‘tsamar’ da ke tsakanin gwamna Obaseki da Oshiomole ta kara fito wa fili. Sai kuma ga shi yanzu jam’iyyar PDP mai adawa a jihar ta ce ta ga ya dace ahau teburin sasanci domin ceto jihar daga abin da ka iya biyowa baya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply