Home Labarai Jihar Gombe ta kirkiro Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida

Jihar Gombe ta kirkiro Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida

78
0

Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya da ke Arewa Maso Gabashin Nijeriya ya furta cewar gwamnatin sa ta amince da kirkiro ma’aikatar tsaron cikin gida da gyaran da’a a jihar domin kula da aikace aikacen dogarawan hanya wato jami’an kula da tuki na jiharsa. Haka kuma za’a  dorawa ma’aikatar alhakin gyara halin yan daba da ke cikin Al’umma.

Yahaya ya bayyana hakan ne a yayin da yake taron manema labaru a cikin wani yanki na bikin cika kwanaki 100 a ofis.

A cewar sa, ma’aikatar za ta lura da aikace aikacen dogarawan hanya na jihar. Ana sa ran kuma wannan mataki zai taimakawa harkar samar da tsaro a jihar ta Gombe.  Gwamnan  ya ce gwamnatin da ta gabata ce ta kirkiro ayyukan jami’an kula da tukin domin hidimta wa alumma.

Yahaya ya kuma ce gwamnatin sa zata kirkiro hukumar da za ta rinka bayar da horo ga matasa da dogarawan hanya din domin shirya su akan yiwuwar daukar su aikin jami’an tsaro a matakin tarayya irinsu aikin soja da dan sanda da imagireshin da sibil-difense da sauransu.

Ya kara da cewa a da dogarawan hanya din ba su da wata dokar da ke kare su, to amman kirkiro sabuwar ma’aikatar zai ba su kariya, kuma a karkashin hukumar za’a basu horo na musamman  kuma hakan zai sa su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply