Home Coronavirus Jihar Kaduna ta tsawaita dokar kulle har bayan sallah karama

Jihar Kaduna ta tsawaita dokar kulle har bayan sallah karama

179
0

Gwamnatin jihar Kaduna a yammacin Lahadin nan ta ce ta kara kwanaki 30 na a ci gaba da zama a gida da daukar matakan kariya daga coronavirus.

A cikin sanarwa mai sahun Muyiwa Adekeye jami’in yada labarai na gwamna Elrufai, gwamnati ta ce babu wanda aka yarda ya fito waje don yin wata sabga madamar shi ba ma’aikacin asibiti ko mai kashe gobara ko mai sayar da magunguna ko dan jarida ko jami’in tsaro ko mai gidan mai bane. Gwamnati ta ce ba ta bukatar wani matafiyi ya ratso jihar, idan kuma har ya shigo to za a killace shi na tsawon makonni biyu.

Muyiwa ya  lissafa hukuncin wadanda suka karya dokar a cikin jihar Kaduna da suka hada da; cin mutum tara ko tura mutum gidan yari ko kuma idan abin hawa ne yake da shi a kwace shi.

Gwamnati ta ce a yanzu rana daya ta ware a cikin mako da jama’a za su iya fita sayen abinci sabanin tsohuwar dokar da ta amince a rinka fita a ranakun Talata da Laraba, yanzu ranar Laraba ce kadai mahukumta suka amince mazauna Kaduna su fita waje.

Gwamnatin ta ce za ta ci gaba da rufe Kaduna har sai ta yi galaba a kan cutar coronavirus.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply