Gwamnatin jihar Kano za ta kashe sama da Naira Biliyan ₦2.3bn domin aikin tashar dakon kaya a Zawachiki cikin ƙaramar hukumar Kumbotso.
Wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labaran jihar Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Asabar, ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da ciwo bashin Euro Miliyan €684,100,100 domin aikin da kuma gyaran hanyoyin jiragen ƙasa.
Wannan mataki da ya zo a lokacin zaman majalisar zartaswar karo na 12 a gidan gwamnatin jihar, ya kuma amince da kashe Naira Miliyan ₦429,248,588 domin aikin allurar riga-kafi na shekarar 2020.
