Home Sabon Labari Jihar Katsina: Agajin gaggawa ga yan gudun hijirar barayin shanu

Jihar Katsina: Agajin gaggawa ga yan gudun hijirar barayin shanu

83
0

Daga Abdullahi Garba Jani

 

Hukumar kai daukin gaggawa a jihar Katsina, ta kai agajin kaya ga wasu al’ummonin da rikicin barayin shanu ya daidaita a kananan hukumomin Kankara da Faskari a cikin jihar.

Shugaban hukumar Alh Babangida Nasamu ya ce, kayan da aka samar sun hada da buhuna 300 na shinkafa, buhuna 30 na wake, buhuna 40 na gero.

Sauran su ne jarkokin man girki 25, katifu da tabarmi 1000, da bandir daya na barguna da kuma katon-katon na taliyar Spaghetti ga kowace karamar hukuma.

Al’ummomin da suka amfana da kayan sun hada da na Kogo, Kafi, Magami, Bangi, Raba da Unguwar Tsamiya cikin karamar hukumar Faskari.

Sai na Zango, Pawwa, Shirere, Gurbi, da ‘Yar Tsamiya cikin karamar hukumar Kankara.

Babangida Nasamu ya ce ba wai hukumar na biyan diyyar asarorin da al’ummomin suka yi ba, tana yi ne don jin kai gare su, samu sa’ida a lamurransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply