Home Sabon Labari Jihar Kebbi: Gwamna Bagudu ya sauke shugabannin kananan hukumomi

Jihar Kebbi: Gwamna Bagudu ya sauke shugabannin kananan hukumomi

97
0

 

Gwamna Atiku Bagudu na jihar kebbi a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Abubakar Muazu Dakingari ya fitar a ranar Laraba ya rushe wa’adin shugabannin kananan hukumomi guda 21 da ke jihar.

Gwamna Bagudu ya dauki wannan mataki ne bayan da waadin zababbun shugabannin kananan hukumomin ya kare a ranar Laraba 24.07.2019.  Da ma tunda farko majalisar dokokin jihar ta Kebbi ta kayyade shekaru biyu a matsayin wa’adin shugabannin kananan hukumomin jihar kamar yadda kundun tsarin mulki ya ba su dama.

A sanarwar sauke shugabannin, gwamna Bagudu ya yi musu fatan alheri da godiya akan irin kokarin da suka yi wurin ciyar da jihar gaba.

Bayanai sun nuna cewa tuni gwamnati ta fitar da ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa a matsayin ranar gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomin na jihar Kebbi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply