Mahukuntan jihar Kebbi sun kaddamar da wani shirin tallafin dabbobi kusan 2,778 ga Fulani makiyaya, da kuma abincin su domin inganta rayuwar su a duk fadin jihar.
Shirin dai an kaddamar da shi ne a Karamar Hukumar Maiyama dake jihar, inda makiyayan suka samu tallafin Tumaki, Awaki, Kaji, da kuma Shanu sai kuma abincin dabbobin da kuma Naira 40,000 tare da wayoyin hannu.
Haka kuma an kaddamar da shirin yin Madarar Youghourt ga matan makiyayan don suma su sami abun dogaro da kai.
Kwamishinan kula da dabbobi da kiwon kifi na jihar Kebbi Alh. Aminu Garba Dandiga ya ce tsare-tsare kusan bakwai suka fito da su na tallafawa makiyayan jihar.
