Home Labarai Jihar Kebbi za ta tura ɗalibai 300 karatu a waje

Jihar Kebbi za ta tura ɗalibai 300 karatu a waje

21
0

Gwamnatin jihar Kebbi za fa tura ɗalibai 300 a ƙasashen India, Turkey da Cyprus domin karatu a fannoni daban-daban da suka haɗa da likitanci, kimiyyar lafiya da injiniya.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Farfesa Mukhtar Bunza ya bayyana haka, a lokacin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar ɗaliban jihar na ƙasa NUKESS da ya gudana ranar Lahadi, a kwalejin koyon aikin jinya da ke Birnin Kebbi.

Bunza wanda Babbar Sakatariya a ma’aikatar Hajiya Halima Dikko ta wakilta, ya ce saboda muhimmancin ilimi ga ci gaban al’umma, ya sanya gwamnatin Atiku Bagudu ta ba ɓangaren muhimmanci, tare da samun nasarori masu yawa a kai.

Ya ce tura ɗaliban sama da 300 karatu a ƙasashen waje, ya faru ne sakamakon yarjejeniyar da jihar Kebbi ta cimma wa da wasu ƙasashen.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply