Hukumar kula da jami’o’i ta Nijeriya ta ba jihar Kogi lasisin gina sabuwar Jami’a mallakin jihar.
Da yake karɓar lasisin daga hannun babban sakataren NUC Farfesa Abubakar Rasheed a Abuja, ranar Talata, Gwamnan jihar Yahaya Bello, ya ce za a gina jami’ar wadda za ta kasance ta kimiyya da fasaha ce a garin Osara da ke Kogi.
Farfesa Rasheed, ya ce an bada lasisin ne domin bada damar inganta ilimin kimiyya da fasaha, injiniya da kuma lissafi tare da bincike da kiwon lafiya da kuma sauran ɓangarori masu alaƙa, a Nijeriya.
A nasa jawabin gwamna Bello, ya ce an ƙirƙiro jami’ar ne musamman don horas da ɗalibai kan yadda za a ci moriyar albarkar da Allah ya horewa Nijeriya da kuma jihar Kogi kususan.
