Home Labarai Jihar Kwara za ta maye gurbin malaman da ta kora da wasu

Jihar Kwara za ta maye gurbin malaman da ta kora da wasu

308
0

Gwamnatin jihar Kwara ta fara aikin daukar malaman makaranta 2,701 a makarantun jihar.

Ma’aikatar ilimi da ci gaban jama’a ta fadi haka a wata sanarwa da sakataren yada labaran ma’aikatar Yakubu Ali-Agan ya fitar ranar alhamis, yana mai cewa sabbin malaman su ne za sum aye gurbin malamai 2,414 da ke karkashin hukumar ilimin bai daya ta jihar SUBEB, da gwamnatin jihar ta kora.

Sanarwar ta ce 2,00 daga cikin malaman za a dauke su ne musamman saboda wasu darussa da ake bukata karkashin hukumar kula da malamai ta TESCOM.

Sanarwar ta ce za a bude shafin intanet inda masu neman aikin za su cika bayanansu a ranar 3 ga watan Janairun 2021, kafin daga bisani a yi wa wadanda za daukar jarabawar tantancewa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply