Daga Abdullahi Garba Jani
Kusan yara almajirai 13,000 ne aka saka a makarantun boko a karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya.
Kazalika, akwai karin wasu yara 8,000 da suka bar zuwa makarantun boko, amma aka maida su a yankin.

Sarkin Keffi Dr Shehu Yamusa, wanda shi ne ya assasa tsarin karatun bokon almajirai a jihar ya ce masarautar ta yanke shawarar kidayar almajirai da yaran da ba su zuwa makarantun boko a yankin a wani mataki na dakile yawon barace-barace a tsakanin kananan yara.
Sarkin ya ce tuni ya kafa wani kwamiti don magance matsalar tare da bukatar sauran masarautu da su rika bin tsarin don dakile yawon bara a tsakanin yara.
