Home Sabon Labari Jihar Nasarawa: Kananan  hukumomi 9 cikin 13 sun kasa biyan albashi.

Jihar Nasarawa: Kananan  hukumomi 9 cikin 13 sun kasa biyan albashi.

81
0

Daga Hannatu mani Abu

 

Ma’aikatan gwamnati a kananan hukumomin da abin ya shafa na cikin tsaka mai wuya. Gwamnan jihar Nasarawa da ke tsakiyar Nijeriya shi ne ya sanar da cewa kananan hukumomi 9 cikin 13 dake jiharsa na fusakantar karancin kudade  a daidai lokacin da ma’aikata suke ta zaman jiran tsammanin biyansu albashin watan Yuni amma suka ji shiru.

 

Abdullahi yace kananan hukumomin da ba za su iya biyan ma’aikata albashin ba sun tsinci kansu a wannan hali ne saboda karancin kudin shiga, wato kudin haraji da gwamnati ke tarawa. Ya ce wasu daga cikin su sun nemi da ya taba kudin manyan ayyuka, capital project, don ya basu su bayar da albashi amma dai bai ba da wannan dama ba. Ya ce tun doka ta ce a ba kananan hukumomi kudinsu ,babu dalilin shi ma yanzu a sa shi ya kaucewa aiki da doka.

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa

Sai dai duk da haka gwamnan ya nuna damuwarsa akan halin da ma’aikata suka shiga sakamakon rashin samun albashinsu. Ya ce yana mai ba su hakurin wannan yanayi da aka shiga.

 

Dama dai gwamnonin jihohi sun sha yin kashedin cewa idan aka ba kananan hukumomi kudadensu ba tare da sunyi hadin gwiwa da jihohi ba to wasu ba za su iya biyan albashi ba. A yanzu da aka fara samun irin wannan labari daga jihar Nasarawa za’a iya cewa wancan hasashe na su ya fara zama gaskiya.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply