Home Labarai Jihar Oyo: Dukiyar gwamna Makinde ta kai Naira Bilyan 50

Jihar Oyo: Dukiyar gwamna Makinde ta kai Naira Bilyan 50

124
0

Kungiyar nan mai yaki da cin hanci ta SERAP a Nijeriya ta ce gwamnan jihar Oyo Seyin Makinde ya cancanci  yabo bayan da ya fitar da bayanan dukiyar da ya mallaka a rayuwa.

 

SERAP a cikin sanarwar da Kolawole Oluwadare mataimakin shugaban ta ya fitar ya kuma aike wa jaridun Nijeriya ciki har da DCL Hausa ta ce bayan da gwamnan na jihar Oyo ya bayyana dukiyar da ya mallaka a wurin hukumar tabbatar da da’ar ma’aikata sai gwamnan ya bayar da umarnin a fitar da wannan bayani don jama’a su san ko nawa ya mallaka kafin ya hau karagar mulki.

Kolawole Oluwadare mataimakin shugaban SERAP

Biyo bayan wannan mataki SERAP ta yaba masa kuma ta bukaci sauran gwamnoni 35 na Nijeriya su yi koyi da gwamna Makinde wurin wallafa  bayanan kadarorinsu.

Mr. Kolawole ya ce lokaci ya yi da gwamnoni za su daina fakewa da cewa wai bayanan dukiyarsu sirri ne, alhali jama’a nada kishin jin labarinsu. Ya ce idan har suna son tabbatar da gaskiya da adalci to su fitar da bayanan kadadorinsu a yanzu tun kafin su dade akan karagar mulki.

A fahimtar SERAP wallafa wannan bayanai zai takaita zargin almundahana da talakawa ke ma gwamnoni. Kazalika zai bada dama cikin sauki a gane ko gwamna ya wawuri kudin jama’a ko kuma a’a.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply